Makaman nukiliya

Yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya, yarjejeniya ce, da aka ƙirƙirota domin iyakance yaɗuwar makaman nukiliya a duniya, kuma ta samo asali ne shekara guda bayan da Amirka ta ƙaddamar da harin makaman nukiliya a Hiroshima da Nagasaki a shekarar 1945. Tun daga wannan lokaci ne Amirkan ta ƙuduri aniyar hana sayarwa ko kuma bayar da makaman nukiliya ga wata ƙasa.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Tashar nukiliya ta ƙasar FaransaShekaru 23 da yin haka sai ƙasashen duniya suka shiga yin yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa akan hana cinikin makaman nukiliya tsakanin ƙasashen duniya. Wannan ne ya sa a ranar 1 ga wata Yulin 1968, aka ƙaddamar da yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya, domin ƙasashen duniya su ci gaba da rattaba hannu a kowanne lokaci. Kuma yanzu haka akwai kasashe 189 da tuni suka rattaba hannun akan amincewa da wannan yarjejeniya. Kodadai biyar daga cikin su sun mallaki makaman nukiliya ɗin.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Tashar nukiliya ta ƙasar BirtaniyaƘasashen da suka rigaya suka ratabba hannun amincewa da wannan yar jejeniya amma kuma sun mallaki makaman nikiliya sun haɗa da ƙasar Amirka da Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma Chaina, wanda kuma sune ƙasashen da ke da wakilcin dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Tukwanen sanyaya nukiliya na ruwa a ƙasar AmirkaDaga cikin ƙasashe masu cikakken 'yanci a duniya, ƙasashe huɗu ne kaɗai ba su sanya hannu akan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliyar ba, kuma sun haɗa da ƙasar Indiya da Isra'ila da Pakistan da kuma Koriya ta Arewa. Inda ƙasar Indiya da Pakistan da Koriya ta Arewa duk sun fito fili sun yi gwajin makaman nukiliyar na su a sarari. Kuma sun bayyana ƙarara cewa, sun mallaki makaman nukiliya. Ita kuwa Isra'ila wani salo ta ɗauka na jirwaye da kamar wanka, ba ta dai fito ƙarara ta nuna nufinta a game da shirinta na makaman nukiliya ba.

Ƙasashen Ireland da Finland dai, su ne suka baiwa duniya shawarar kafa wannan yarjejeniya, su ne kuma ƙasashe na farko da suka fara rattaba hannun amincewa da ita. Yarjejeniyar dai ta ƙunshi gabatarwa da kuma sassa guda tara.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Ofishin harkokin nukiliya na ƙasar ChainaAna dai sabunta yarjejeniyar duk bayan shekaru biyar. Kuma duk da cewa, da farko an tsara yarjejeniyar za ta kasance ne tsawon shekaru 25, to amma ƙasashen da suka sanya hannun gabakiɗayansu sun amince da a bar ƙofa buɗe ba tare da iyakancewa ba, ga duk ƙasar da take buƙatar sanya hannu a yarjejeniyar nan gaba.

Other Languages
Afrikaans: Kernwapen
Alemannisch: Kernwaffe
aragonés: Arma nucleyar
العربية: سلاح نووي
asturianu: Arma nuclear
azərbaycanca: Nüvə silahı
башҡортса: Ядро ҡоралы
žemaitėška: Kondoulėnis gėnklos
беларуская: Ядзерная зброя
беларуская (тарашкевіца)‎: Ядзерная зброя
български: Ядрено оръжие
brezhoneg: Arm nukleel
català: Arma nuclear
čeština: Jaderná zbraň
Cymraeg: Arf niwclear
Deutsch: Kernwaffe
Ελληνικά: Πυρηνικό όπλο
español: Arma nuclear
eesti: Tuumarelv
euskara: Arma nuklear
suomi: Ydinase
français: Arme nucléaire
Frysk: Kearnwapen
贛語: 核武器
galego: Arma nuclear
गोंयची कोंकणी / Gõychi Konknni: अणुबॉंब
हिन्दी: परमाणु बम
interlingua: Arma nuclear
Bahasa Indonesia: Senjata nuklir
íslenska: Kjarnorkuvopn
italiano: Arma nucleare
日本語: 核兵器
қазақша: Ядролық қару
한국어: 핵무기
Кыргызча: Ядролук курал
Lëtzebuergesch: Atomwaff
latviešu: Kodolieroči
македонски: Нуклеарно оружје
മലയാളം: ആണവായുധം
Bahasa Melayu: Senjata nuklear
မြန်မာဘာသာ: အဏုမြူ လက်နက်
नेपाली: परमाणु बम
नेपाल भाषा: आणविक ल्वाभः
Nederlands: Kernwapen
norsk nynorsk: Atomvåpen
occitan: Arma nucleara
ਪੰਜਾਬੀ: ਨਿਊਕਲੀ ਬੰਬ
Pälzisch: Kernwaffe
پنجابی: ایٹم بمب
português: Bomba nuclear
română: Armă nucleară
संस्कृतम्: अण्वस्त्रम्
سنڌي: ائٽم بم
srpskohrvatski / српскохрватски: Nuklearno oružje
Simple English: Nuclear weapon
slovenčina: Jadrová zbraň
slovenščina: Jedrsko orožje
српски / srpski: Нуклеарно оружје
Seeltersk: Käädenwoape
Basa Sunda: Pakarang nuklir
svenska: Kärnvapen
Kiswahili: Bomu la nyuklia
తెలుగు: అణ్వాయుధం
Türkçe: Nükleer silah
татарча/tatarça: Атом-төш коралы
українська: Ядерна зброя
oʻzbekcha/ўзбекча: Yadro quroli
Tiếng Việt: Vũ khí hạt nhân
吴语: 核武器
中文: 核武器
Bân-lâm-gú: He̍k-chú bú-khì
粵語: 核武